Taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adama, wanda aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin daga ranar 10 zuwa ranar 11 ga watan nan, mai taken “Kiyaye bambancin wayewar kan al’adun bil’adama don samun zaman lafiya da ci gaban duniya”, ya ja hankalin baki daga kasashe da yankuna 140 da suka hada da ‘yan siyasa da ministocin gwamnatoci da kuma wakilan bangarori daban daban, inda suka yi musayar ra’ayin tare da cimma matsaya a fannoni da yawa, da kuma fitar da sanarwar Beijing, bayan kammala taron.
Sanarwar ta bayyana cewa, mu’amalar wayewar kai muhimmin karfi ne wajen inganta ci gaban wayewar kan bil’adama da bunkasuwar zaman lafiyar duniya. Kuma ya kamata kasashe da kabilu daban-daban su tabbatar da mutunta juna, su ba juna goyon baya kan hanyoyi da tsarin samun ci gaba da suka zaba da kansu, da kiyaye bambancin al’adu, da inganta mu’amala, da tattaunawa, da zaman jituwa tsakanin wayewar kai daban-daban.(Safiyah Ma)