Da maraicen yau Laraba 9 ga wata ne, a wajen taron kolin Wuzhen na babban taron yanar gizo na duniya na shekara ta 2022, cibiyar nazarin kafar yanar gizo ta intanet ta kasar Sin, ta fitar da takardar bayani kan rahoto game da ci gaban yanar gizo ta kasar Sin na shekara ta 2022, da rahoto game da ci gaban yanar gizo ta duniya na shekara ta 2022.
Tun daga shekara ta 2017, an fitar da irin wannan takardar bayani zuwa ga duk fadin duniya a cikin jerin shekaru shida, matakin da ya kasance wani muhimmin bangare na babban taron yanar gizo na duniya.
Takadar bayanin, wani muhimmin sakamakon nazari ne da aka yi, wadda cibiyar nazarin kafar yanar gizo ta intanet ta kasar Sin, da sauran wasu cibiyoyin kwararrun nazarin bangaren yanar gizo na gida da na waje suka tsara cikin hadin-gwiwa, inda aka nuna sabon ci gaba, da sabbin nasarorin da aka samu a bangaren bunkasa harkokin yanar gizo ta intanet. (Murtala Zhang)