A ranar 19 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da takardar matsayar kasar Sin a taron kolin MDD kan makoma da muhawarar babban taron MDD karo na 79.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ne ya bayyana hakan a taron manema labarai, inda ya ce, takardar ta bayyana cikakkiyar matsayar kasar Sin game da zaman lafiya da tsaro, da ci gaba mai dorewa, da kare hakkin bil Adama, da musayar al’adu, da kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da yin gyare-gyare a harkokin mulki na duniya da dai sauransu, kana takardar ta yi kira ga kasashen duniya su yi aiki tare wajen aiwatar da shirin ci gaban duniya, da shirin tsaro na duniya, shirin wayewar kai na duniya, da sa kaimi ga gina al’umma mai makomar bai daya ga bil Adama. (Yahaya)