Yau Talata, an fitar da tsarin manhajar wayar salula na farko na kasar Sin a hukumance, wato tsarin da aka yiwa lakabi da HarmonyOS na kamfanin Huawei, kuma shi ne tsari na uku mafi girma a duniya, bayan tsarin manhajojin iOS na kamfanin Apple, da na Android.
Bisa tsarin manhajar HarmonyOS da aka fitar a wannan karo, an samu nasarar yin duk wani bincike da kai yayin samar da manhajar, kuma an kyautata inganci, da tsaro a bayyane.
A halin yanzu, an riga an kaddamar da manhajoji, da hidimomi na HarmonyOS fiye da nau’o’i 15,000, wadanda suka shafi sana’o’i guda 18. Adadin na’urorin dake amfani da tsarin manhajar ya zarce biliyan 1, kuma masu amfanin manhajoji da suka yi rajista sun kai miliyan 6.75. (Safiyah Ma)