A kwanakin nan ne, kwamitin kolin JKS da majalisar gudanarwar kasar Sin, suka ba da shawarar yin gyare-gyare ga jam’iyya da hukumomin gwamnati, tare da ba da sanarwar bukatar dukkan yankuna da sassan kasar da su aiwatar da shi bisa la’akari da hakikanin yanayin da ake ciki.
Shirin sake fasalin jam’iyya da hukumomin kasa ya nuna cewa, manufar zurfafa gyare-gyaren jam’iyya da cibiyoyi na kasa shi ne, gina tsarin aiki na jam’iyya da hukumomin gwamnati bisa tsari na kimiyya da daidaito, tare da gudanar da aiki yadda ya kamata.
Canje-canjen da abin ya shafa, sun hada da kafa kwamitin kolin kula da harkokin kudi, kwamitin koli na kimiyya da fasaha, da hukumar tattara bayanai ta kasa, da sauransu. (Mai fassarawa: Ibrahim)