A kwanan nan ne aka fitar da motar daukar mara lafiya ta farko mai ISO na ma’auni na kasa da kasa, wanda tawagar bincike karkashin jagorancin kwararrun Sinawa suka tsara, mai suna motar asibiti mai dakin kebance mara lafiya wato “Negative Pressure Ambulance Medical Cabin Technical Specifications”.
Wadannan motocin asibiti masu dakin kebance mara lafiya suna da kayan aikin jinya masu muhimmanci, galibi ana amfani da su don kebe mara lafiya cikin aminci yayin da ake jigilarsu, kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen kula da cututtuka daban-daban na numfashi. Wannan ma’auni na kasa da kasa ya gabatar da bukatun fasaha a karon farko wanda ya kamata a samar a cikin irin wadannan motocin asibiti masu dakin kebance mara lafiya, kuma yana tabbatar da cewa za a iya bayar da karin hidimomin jinya da kayayyakin aikin dake cikin motar a yayin da ake jigilar marasa lafiya.
Fitar da wannan ma’auni ya gabatar da kayyadaddun kayayyakin aiki da ake bukata a cikin wadannan motocin asibiti masu dakin kebance mara lafiya, wanda zai zama abin koyi ga kasashen duniya, kuma zai yi tasiri mai kyau a kan rigakafi da kula da cututtukan numfashi a duniya. Kwararru daga kasashen Sin, Faransa, Italiya da sauran kasashe suka yi hadin gwiwa wajen bincike da tsara wannan ma’auni. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp