Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a kasar Faransa a halin yanzu, an yi bikin kaddamar da wani shirin bidiyo da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya tsara a birnin Paris a yau Litinin, mai suna “Labarun Da Xi Jinping Ya Fi So”. Shugaban kwamitin kula da kundin tsarin mulkin kasar Faransa, wanda kuma shi ne tsohon firaministan kasar, Laurent Fabius, da tsohon firaministan kasar, kana shugaban gidauniyar La Fondation Prospective & Innovation ko kuma FPI a takaice, Jean-Pierre Raffarin, sun taya murnar kaddamar da bikin. Kaza lika, wasu muhimman kafafen yada labarai na Faransa, ciki har da DailyMotion, da gidan talabijin na Euronews sun watsa wannan shirin bidiyon.
Mataimakin shugaban sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG, Shen Haixiong, da tsohon ministan kula da muhallin Faransa, kana tsohon mataimakin sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Brice Lalonde, sun gabatar da jawabai a wajen bikin, inda kuma suka kaddamar da shirin tare da shugaban rukunin darektocin gidan talabijin na Euronews. Shugaban rukunin sada zumunta tsakanin Sin da Faransa na majalisar dokokin kasar Faransa, Éric Alauzet shi ma ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi. (Murtala Zhang)