A ranar 23 ga watan Augusta aka gabatar da shirin musayar al’adu mai taken “Echoes of Peace” a birnin Mexico na kasar Mexico. Cikin jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, Mr.Shen Haixiong, shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya ce yana farin cikin gayyatar baki su hallarci wajen gabatar da shirin domin a waiwayi tarihi tare a kuma fahimci abun da ya faru, wanda tasirinsa ya keta lokaci da yankuna.
Ya ce a shirye kafar CMG take ta zurfafa hada hannu da abokan hulda na kasa da kasa wajen hada kai domin shawo kan kalubale da neman ci gaba ta hanyar hadin gwiwa. (Fa’iza Mustapha)