Majalissar gudanarwar kasar Sin, dake zama majalisar zartaswar kasar, a yau Talata ta gabatar da wani shiri kan yin gyare-gyare ga hukumominta, ga taron farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, domin tattaunawa a kai.
Kasar Sin na shirin sake fasalin ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar, domin kara ware kudade don shawo kan kalubalen da ake fuskanta kan muhimman fasahohi, da hanzarta dogaro da kai a fannin kimiyya da fasaha.
Ma’aikatar da aka sake yi wa fasali, za ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta sabon tsarin wayar da kan al’ummar kasar, a wani mataki na samun ci gaba a fannin fasaha, da inganta fasahar kere-kere, da saukaka aiwatar da ci gaban fasahar kere-kere, da daidaita kimiyya da fasaha tare da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Haka kuma, kasar Sin za ta kafa hukumar kula da harkokin kudi ta kasa. bisa shirin. Kai tsaye a karkashin majalisar gudanarwa ta kasa, hukumar da aka gabatar za ta kasance mai kula da harkokin hada-hadar kudi, amma ban da bangaren takardun shaidar kudi.
Kasar Sin za ta kafa ofishin tattara bayanai na kasa. Ofishin da ake shirin kafawa, wanda zai kasance karkashin kulawar hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasa (NDRC), shi ne zai dauki nauyin inganta ci gaban cibiyoyi masu alaka da bayanai, da hada kai, raba, bunkasa da aiwatar da albarkatun bayanai, da ciyar da shirin gaba, da gina Sin ta zamani, da tattalin arziki da al’umma ta zamani, da dai sauransu.(Ibrahim)