Jiya Laraba, a taron majalisar hakkin bil Adama ta MDD karo na 57, an cimma matsaya daya wajen zartas da kudurin tuna da cika shekaru 30 da zartas da Sanarwar Beijing da Tsarin dokoki game da yawan mutane da neman ci gaba. Wannan kudurin da kasar Sin ta gabatar a madadin kasashen Denmark da Faransa da Kenya da kuma Mexico, ya samu goyon baya daga kasashe guda 112.
Zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin Geneva na MDD, kana wakilin kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, Chen Xu, ya bayyana cewa, a shekarar 1994, an zartas da Sanarwar Beijing da Tsarin dokoki game da yawan mutane da neman ci gaba a babban taron matan kasashen duniya karo na 4 da aka yi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, lamarin da ya kasance muhimmin matakin raya harkokin mata a kasashen duniya. Yanzu, shekaru 30 sun riga sun wuce, matsayin mata ya daga matuka cikin kasa da kasa, amma, ana fuskantar kalubaloli da dama ta fuskar aiwatar da Sanarwar Beijing bisa dukkan fannoni. Shi ya sa, kudurin da aka zartas a wannan karo, zai kara kwarin gwiwa wajen ci gaba da aiwatar da Sanarwar Beijing, ya kuma nuna fatan bangarori daban daban wajen neman adalci a tsakanin mabambantan jinsi, da kuma yin hadin gwiwa domin fuskantar kalubalolin da abin ya shafa.
Wakilai na kasashen Faransa, Gambia, Sudan da kuma Japan sun ba da jawabai a lokacin da aka zartas da kudurin, inda suka nuna godiya ga kasar Sin, da ta gabatar da wannan muhimmiyar shawara a madadin kasashensu, yayin da yi kira ga kasashen duniya da su bi Sanarwar Beijing, ta yadda za a inganta ayyukan kiyaye hakkin matan kasa da kasa. (Mai Fassara: Maryam Yang)