Bayan isar shugaban kasar Sin Xi Jinping birnin Astana, fadar mulkin kasar Kazakhstan, domin halartar taron koli karo na biyu tsakanin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, a jiya Litinin, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Kazakhstan, suka gudanar da bikin mu’amalar jama’a da al’adu a tsakanin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, a cibiyar shugaban kasar Kazakhstan.
Shugaban kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, ya aike da wasikar taya murnar gudanar da bikin, inda ya yi fatan cimma nasarar gudanarwar da bikin, tare da yin maraba da gaisuwarsa ga mahalarta bikin.
A yayin bikin, an gabatar da kiran karfafa hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labarai a tsakanin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, yayin da kuma aka gabatar da shirye-shiryen talabijin da dama, wadanda aka dauka bisa hadin gwiwar kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, kana, an cimma nasarar watsa labarai bisa hadin gwiwar kafofin sassan biyu, bisa babban jigon “Tafiye-Tafiye A Tsakiyar Asiya”.
Wakilai sama da 150 daga kasar Sin da kasashe 5 a yankin tsakiyar Asiya, sun halarci wannan biki, wanda ya karkata ga harkokin dake shafar siyasa, da tattalin arziki, da al’adu, da kafofin watsa labarai, da kuma aikin ba da ilmi. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp