Jiya Alhamis, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a kasar Cambodia, CMG da hukumar yada labarai ta Cambodia, da ta raya ala’du da fasahohi da yawon bude ido, da kuma kwalejin nazari karkashin masaurantar kasar sun gabatar da bikin musanyar al’adun al’ummun kasashen biyu cikin hadin gwiwa a Phnom Penh, fadar mulkin kasar. Inda aka fara aiwatar da tsarin abokantaka na kafofin yada labaran kasashen biyu, da gabatar da shirye-shiryen cudanyar wayewar kan al’ummun kasashen biyu, kana da bikin nuna fina-finai a budadden wuri karo na 10.
Baya ga haka kuma, CMG ta kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa da hukumomin gwamnatin kasar, da kafofin yada labarai na kasar. Shugaban jam’iyyar jama’ar Cambodia wato CPP, kana shugaban majalisar dattawan kasar Samdech Techo Hun Sen ya aike da wasikar taya murna, don bayyana kyakkyawan fata ga samun ci gaba mai armashi a cikin wadannan ayyuka. Wakilan kasahen biyu su fiye da 200 daga bangaren siyasa, da tattalin arziki, da al’adu, da fasahohi, da kuma kafofin yada labarai sun halarci wannan biki.
Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi, inda ya ce CMG ta hada gwiwa da mabambantan bangarori ta fuskar al’adu, albarkacin ziyarar aikin Xi Jinping a wannan karo. Lamarin da ya taka rawar gani wajen bunkasa dadadden dankon zumuncin al’ummun kasashen biyu, da gaggauta aikin kyautata tsarin mu’ammala da yada labarai tsakanin mabanbantan kasashe karkashin manufar dunkulewar duniya, da kaiwa ga matsaya daya ta samun bunkasuwa cikin lumana, kana da ingiza karfin kasashe masu tasowa a bangaren bayyana matsaya da ra’ayinsu a dandalin duniya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp