Gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Serbia, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG da babban gidan talabijin da rediyo na kasar Serbia, sun shirya wani bikin musayar al’adu, ranar Talata a Belgrade, mai taken “ Sin da Serbia tamkar makwabta ne dake da tazarar dubban mila milai”. Shugaban kasar Serbia Aleksandar Vucic, ya gabatar da jawabi ta kafar bidyo domin taya murnar gudanar bikin cikin nasara. (Fa’iza Mustapha)