Da safiyar yau Litinin, aka gudanar da cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na 20 a nan birnin Beijing. A madadin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da rahoton aiki ga mahalarta zaman. Kuma ya yi karin haske kan daftarin tsarin shawara kan shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15. (Amina Xu)