A ranar Juma’a ne an gudanar da dandalin matasan Sin da Afirka kan ayyukan sa kai, wanda aka yiwa take da “Hadewa, da karfafa gwiwar matasa masu ayyukan sa kai, domin gina ci gaban hadin gwiwar Sin da Afirka”.
Masu gabatar da makala sun yi musayar ra’ayi, game da ci gaban Sin, da hadin gwiwar kasa da kasa a fannin ayyukan sa kai da matasa ke gudanarwa, da manufofin nahiyar Afirka masu nasaba da bunkasa ci gaban matasa, da ma kwarewar nahiyar a fannin ayyukan sa kai na matasa.
A cewar mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar matasan kasar Sin Xu Xiao, dandalin ya samar da wata sabuwar dama ga matasa, ta shiga a dama da su a ajandojin bunkasa ci gaban duiya, da manufofin raya duniya na kasa da kasa. Xu ya ce kungiyar matasan Sin na da burin karfafa hadin gwiwa da kungiyoyin matasan Afirka masu aikin sa kai, wajen ingiza ci gaban matasan Sin da na Afirka. (Saminu Alhassan)