A yau Talata ne aka gudanar da dandalin tattaunawa, tsakanin kafofin watsa labarai na kasa da kasa karo na 12 a birnin Quanzhou dake lardin Fujian, inda mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwamins ta Sin, kuma shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS, Li Shulei, ya halarci taron ta kafar bidiyo tare da gabatar da jawabi.
Mahalarta dandalin sun yi imanin cewa, ya kamata kafofin watsa labarai na kasa da kasa su karfafa mu’amala da hadin gwiwarsu, da yada ra’ayi da ayyuka na zamanintar da kasashe masu tasowa, da kuma taimakawa kasashe masu tasowa su cimma zamanintarwa tare.
- Sabon Albashi: NLC Ta Fara Yajin Aiki A Jihohi 15 Na Nijeriya
- CMG Ya Gabatar Da Alamar Bayyana Kyakyyawar Fata Ta Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Kasar Sin
Shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, Shen Haixiong, ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, CMG zai ba da gudummawarsa ga inganta gina al’umma mai makomar bai daya ta daukacin bil’adama tare da sauran abokansa.
Dandalin tattaunawar na wannan karo na da jigon “Rawar da kafofin watsa labarai ke takawa yayin mu’amalar al’adu”, kuma kamfanin dillancin faya-fayan bidiyo na kasa da kasa karkashin CMG ne ya dauki nauyin gudanar da shi. (Safiyah Ma)