A ranar Talatar nan 15 ga watan Afrilu ne aka gudanar da wani taron harkokin cudanya da musanya a tsakanin jama’ar kasashen Sin da Malaysia, wanda ke da taken “Hada kai don samun wadata”, wanda rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, watau CMG ya shirya a birnin Kuala Lumpur.
A wajen taron, rukunin na CMG ya cimma yarjeniyoyin hadin gwiwa da dama da kungiyar sada zumunta tsakanin Malaysia da Sin ta kasar Malaysia, da Jami’ar Tunku Abdul Rahman ta Malaysia, da Cibiyar Nazarin Dabarun Bunkasa Yanki ta Malaysia da Babbar Cibiyar nazari ta Zheng He ta kasa da kasa da ke kasar. Hadin gwiwar da aka kulla ya fi mayar da hankali ne a kan musayar ilimi, da ziyarar ma’aikata, da ayyukan gidajen watsa labaru, da bincike na kwararru da sauran fannoni masu alfanu.
Fiye da baki 200 daga bangarorin siyasa, da tattalin arziki, da al’adu, da ilimi da kafofin yada labarai na Malaysia ne suka halarci taron. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp