A daren jiya Asabar, gabannin bikin cika shekara daya da bude wasannin Olympics na lokacin sanyi na 2022 na birnin Beijing, an gudanar da bikin kaddamar da jerin ayyuka, na murnar cika shekara daya, da cimma nasarar gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing.
A jawabinsa ta kafar bidiyo, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa wato IOC Thomas Bach, da farko ya mika sakon taya murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin da Sinanci ga al’ummar kasar. Ya kuma kara da cewa, “Idan aka waiwayi baya, ya kamata kasar Sin ta yi alfahari matuka, kuma idan aka sa ido aka hangi gaba, ya kamata kasar Sin ta kasance mai cike da kwarin gwiwa.”
Mr. Bach ya ce yanzu kayayyakin da aka samar sakamakon wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing sun fara amfanar jama’a, inda duk wuraren wasannin Olympics a bude suke ga jama’a, kuma gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta kafa sabbin ma’auni a fannoni da dama, ciki har da kirkire-kirkiren fasahohin na kiyaye muhalli, da yada salon rayuwa mai inganci, da bunkasa masana’antar wasannin kankara da dusar kankara da dai sauransu.
Mutane masu shiga wasannin Olympics na kasar Sin sun bayyana sabon taken Olympic, wato “Kara sauri, kara tsayi, kara karfi da kara hadin kai’. ”
Tun daga jiya Asabar 4 ga watan nan, an soma gudanar da jerin ayyuka na murnar cika shekara daya, da samun nasarar gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022 a yankunan wasannin uku dake Beijing, da Yanqing, da kuma Zhangjiakou.
Ayyukan da aka kaddamar sun sake ingiza sha’awar jama’a, ga shiga wasannin kankara da na dusar kankara. (Mai fassara: Bilkisu Xin)