A ranar 31 ga Janairu agogon kasar Kenya, an gudanar da shagali kafin bikin bazara na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Nairobi. Taken bikin shi ne “Murnar bikin bazara na kasar Sin da kallon shagalin bikin bazara na CMG”, ta hanyar yin amfani da al’adun bikin bazara a matsayin wata hanyar da za ta sa kaimi ga yin mu’amalar al’adu na kasa da kasa, da sa kaimi ga fahimtar juna game da da wayewar kai. Fiye da baki 200 da suka hada da manyan jami’an MDD da jakadu a MDD ne suka halarci bikin.
Shen Haixiong, shugaban CMG, ya bayyana a cikin wani jawabi na faifan bidiyo cewa, kawo yanzu, an gudanar da shagalin bikin bazara har sau 41 a jere, wanda ya kasance abin tunawa a zukatan masu kallo na wadannan zamani da kuma muhimmiyar kafar yayata al’adu don duniya ta kusanci tare da fahimtar kasar Sin. CMG a shirye yake ya yi aiki tare da abokan Afirka don inganta zamanantarwa da ba da gudummawa ga gina babban al’umma mai makomar bai daya tsakanin Sin da Afirka. (Mai fassara: Yahaya)