A ranar 16 ga watan Janairu bisa agogon birnin New York, an gudanar da wani kwarya-kwaryan biki mai taken “somin-tabin shirye-shiryen murnar bikin bazara da kasa da kasa ke kallo”, na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, a birnin na New York na kasar Amurka.
Yayin bikin, shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta hanyar bidiyo inda ya bayyana cewa, bikin bazara yana daya daga cikin bukukuwa mafi muhimmanci ga al’ummun kasar Sin. Kuma zuwa bana, an gudanar da bikin murnar sabuwar shekarar Sinawa a jere cikin shekaru 42, kana har illa yau bikin ya zama wani nau’i na shirye-shiryen talabijin na al’ada da fasaha dake samun mafi yawan masu kallo a duniya.
Ya kara da cewa, za a yada shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na shekarar bana cikin harsuna 82, ta yadda za a gabatar da al’adu masu kayatarwa da masu kallo na gida da na waje za su ji dadinsu. (Safiyah Ma)