Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya kaddamar da taro mai taken “A rubuce a sama: Labarina na kasar Sin” a birnin Mexico na kasar Mexico a ranar 20 da kuma a birnin Canberra na kasar Australiya a jiya Litinin ga watan nan da muke ciki bisa agogon wurin, don murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin.
Yayin kaddamar da bikin, shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Haka kuma, jakadan Sin dake kasar Zhang Run da shugabar kwamiti mai kula da harkokin Asiya da tekun Pasifik na majalisar dattawa ta kasar Mexico kana tsohuwar shugabar rukunin sada zumunta tsakanin Sin da Mexico na majalisar wakilan kasar Madam Yeidckol Polevnsky, da sauran wakilan kasar fiye da 100 daga bangaren siyaysa da kafofin watsa labarai da kuma malamai da daliban jami’ar kasar mai zaman kanta da na kwalejin Mexico, sun halarci taron.
- Sin Ta Samu Karuwar Mazauna Birane Cikin Shekaru 75
- Tarihin Ci Gaban Sin: Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa
Shen Haixiong kuma ya gabatar da jawab ta kafar bidiyo yayin da aka kaddamar da bikin a Austriliya. Kana jakadan Sin dake kasar Xiao Qian da babban darekta mai kula da aikin zirga-zirgar jiragen sama zuwa ketare da kasuwar yawon bude ido a bangaren gabashin duniya na ma’aikatar yawon bude ido na kasar Australiya Andrew Hogg da sauran jami’an kasar, sun halarci taron. Haka zalika, wakilai kimanin dari daga bangaren siyasa da masana da kafofin yada labarai da Sinawa dake kasar, su ma sun halarci taron.
Mahalarta taron sun kai ga matsaya daya cewa, fahimtar bunkasuwar kasar Sin, ba kawai zai taimaka musu wajen fahimtar yadda kasar ke kokarin zamanintar da kanta ba, har ma zai taimaka wajen karfafa dankon zumunci a tsakanin Sin da wadannan kasashe biyu da ma sauran kasashen duniya, da ma tabbatar da bunkasuwarsu ta bai daya.(Amina Xu)