An gudanar da taron dandalin ciniki tsakanin Sin da Habasha kana taron sa kaimi ga dandalin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa wato CISCE karo na 3 a jiya Litinin a Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha.
Kwamitin sa kaimi ga cinikin Sin da ketare da kwamiti mai kula da harkar zuba jari na Habasha da kungiyar kasuwanci da kungiyar sana’o’in Habasha sun gudanar da taro mai taken “Shiga Habasha: Habaka hadin gwiwar tsarin samar da kayayyaki tsakanin Sin da Afirka” cikin hadin kai. Inda wakilai fiye da 200 daga bangarorin gwamnatoci da ciniki da tattalin arziki da kafofin yada labarai da sauransu suka halarci taron.
Jakadan Sin dake Habasha Chen Hai ya gabatar da wani jawabi, inda ya ce, dandalin CISCE irinsa na farko a duniya dake mai da hankali kan tsarin samar da kayayyaki a duniya, zai samar da wani muhimmin dandali ga mabambantan kamfanonin kasashen duniya wajen habaka kasuwaninsu a ketare da jawo jari daga waje da mu’amalar kimiyya da daga kimar kasashensu da dai sauransu.
Darektan kwamiti mai kula da zuba jari na Habasha Zeleke Temesgen ya ce, a halin yanzu, Sin ta zama daya daga cikin abokai mafi karfi a bangaren ciniki da zuba jari ga Habasha. Yana fatan ’yan kasuwan kasar Sin za su nazarci babbar damar zuba jari a kasarsa, da kafa huldar abokantaka mai karfi da dorewa tsakaninsu, a cewarsa. Yana mai fatan shigowar Sin wannan bangare zai gaggauta bunkasa tattalin arzikin kasar, har ma da samar da karin guraben aikin yi da ingiza samun wadata cikin hadin gwiwa baki daya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp