Yau Laraba, ma’aikatar harkokin wajen Sin da lardin Hainan sun gudanar da taro mai jigon “Ayyukan gida na zamanantar da Sin: Tashar jiragen ruwa ta ciniki cikin ‘yanci ta Hainan, sabon zamani, sabon nauyi, sabbin dammamaki” a nan birnin Beijing.
Bisa gabatarwarsa, taron ya mai da hankali kan babban ci gaba da aka samu, yayin da ake gina tashar jiragen ruwa ta ciniki cikin ‘yanci ta Hainan, wanda hakan ya ci gaba da nuna aniyar Sin ta tsayawa tsayin daka kan inganta gyare-gyare ta hanyar bude kofa, da kuma gina sabon tsari na budadden tattalin arziki mai inganci.(Safiyah Ma)