An gudanar da taron kasa da kasa na tattaunawa kan batun kirkire-kirkire, da bude kofa, da raba damar samun ci gaba a birnin Colombo na kasar Sri Lanka. Kafar CMG ta Sin, da ofishin jakadancin Sin dake Sri Lanka ne suka shirya taron na ranar Talata 28 ga wata.
Yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce cikakken taro na hudu na kwamitin kolin JKS na 20 ya gudana cikin nasara a birnin Beijing, kuma hakan ya shaida muhimmiyar nasarar da Sin ta cimma a sabon zamani. Taron ya kara fayyacewa duniya kudurin kasar Sin na fadada bude kofa ga sassan kasa da kasa bisa matsayin koli, don bude sabon babin hadin gwiwa da cin moriyar juna.
Shen Haixiong, ya ce kafar CMG za ta yi aiki tare da abokan huldarta, wajen aiwatar da manyan shawarwarin hudu da kasar Sin ta gabatar ga kasashen duniya, don raba moriyar dabarun Sin na inganta jagorancin duniya, da kyakkyawar makomar salon Sin na zamanantarwa, da ma kirkire-kirkiren Sin a sabon zamani.
Ya ce, ba za a iya raba ci gaban kasar Sin da na sauran sassan duniya ba, kuma ci gaban duniya na bukatar gudummawar Sin. A shirye muke mu hada hannu tare da ku baki daya, wajen cimma burikanmu tare, da ingiza gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga dukkanin bil’adama, da hada karfi wajen samar da kyakkyawar makoma ta dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan)
 
			



 
							








