A yau Litinin ne aka gudanar da taron manyan jami’ai na dandalin FOCAC karo na 17 a birnin Beijing. Taron na wannan karo ya nazarci, tare da amincewa da kundi mai kunshe da daftarin sakamakon taron masu ruwa da tsaki na FOCAC na 2024, da kuma daftarin ajandar taron ministoci na dandalin karo na 9.
Taron na manyan jami’ai da ya gudana, na da nufin share fagen babban taron masu ruwa da tsaki na FOCAC na 2024, da taro karo na 9 na ministocin dandalin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp