Hukumar da ke yaƙi da laifukan da suka shafi hada-hadar kuɗi a Nijeriya, NFIU, ta ce dokar hana cire tsabar kuɗi daga asussan gwamnati a kowane mataki za ta fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Maris mai zuwa.
BBC ta rawaito cewar hukumar, Nigeria Financial Intelligence Unit (NFIU), duk wani jami`in gwamnati da ya taka dokar zai fuskanci ɗaurin shekara uku a gidan yari ko kuma tarar da za ta kai ninkin kuɗin da ya cira sau uku.
- Dole Gwamnan CBN Ya Gurfana A Gaban Kuliya – Alhaji Ibrahim
- Ya Kamata CBN Ya Saurari Koke-koken Al’umma – Alhaji Ibrahim
Shugaban NFIU, Malam Modibbo Hamman Tukur, ya faɗa wa BBC Hausa cewa tun daga lokacin da gwamnatin Buhari ta fara mulki an cire jimillar garin kuɗi naira biliyan 225 daga asusun gwamnatin tarayya.
“Gwamnatocin jiha ne suka fi cirar kuɗin, inda aka ɗauki garin kuɗi biliyan 700. Gwamnatocin ƙananan hukumomi kuma biliyan 156 kawai suka cira,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp