Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya a ranar Talata ta sanar da cewa, ɗaliban makarantun sakandire na Nijeriya masu karatu a fannin Zamantakewa (Arts) da Kimiyyar Ɗan’adam (Humanities) ba za a ƙara buƙatar su gabatar da kiredit a fannin lissafi a jarabawarsu ta kammala makarantar sakandire (SSCE) ba, wadda Hukumar Jarabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) da Hukumar Jarabawa ta Ƙasa (NECO) ke shiryawa a matsayin sharaɗi na samun shiga jami’o’i da kwalejojin fasaha.
Tsawon shekaru da dama, masu neman shiga manyan makarantu a fannin (Arts) da Kimiyyar ɗan’adam, kamar takwarorinsu na fannin Kimiyya (Sciences), an wajabta musu samun kiredit biyar, ciki har da lissafi da harshen Ingilishi, don samun gurbin karatu a manyan cibiyoyin ilimi.
Wannan kwaskwarimar da aka yi wa tsarin ilimin, an yi ta ne da nufin kawo sauki ga dokokin da aka gindaya wa Ɗaliban Sakandire masu shirin ci gaba da karatu zuwa manyan makarantu da kuma kawar da cikas, tare da kiyaye matsayin ilimi a kasar ta Nijeriya baki daya.