A jiya Alhamis 4 ga watan nan, a birnin Geneva na kasar Switzerland, yayin da majalissar kwamitin kare hakkin bil Adama ta MDD ta amince da halartar kasar Sin, zagaye na hudu na duba batutuwan da suka shafi kare hakkin dan Adama na kasa da kasa, mahalarta zaman sun barke da tafi, kuma da dama daga wakilan kasashe mahalarta sun taya wakilan kasar Sin murnan wannan nasara.
Cikin tsawon shekaru, kasar Sin na ta dora muhimmanci kan kare hakkin rayuwa, da ci gaban al’umma, a matsayin jigon kare hakkin bil Adama, kuma nasarorin ta a fannonin kare hakkin al’umma a bayyane suke ga kowa. Baya ga haka, Sin ta bayar da gudummawa ga kudurorin kare hakkin bil Adama a matakin kasa da kasa, lamarin da ya yi matukar samun karbuwa daga dukkanin bangarori.
Har ila yau, manufofin kasar Sin na hada karfi da karfe wajen gina shawarar “Ziri daya da hanya daya”, sun haifar da gudanar ayyukan hadin gwiwa sama da 3000 a sassa daban daban na duniya, wanda hakan ya taimaka wajen fitar da kusan mutane miliyan 40 daga kangin fatara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)