Babban jami’in ayyukan fasaha, a cibiyar kandagarki da shawo kan yaduwar cututtuka ta nahiyar Afirka ko Africa CDC, mista Joseph Wangendo, ya ce hadin gwiwa mai karko tsakanin Sin da kasashen Afirka, ya haifar da muhimmin mataki na kyautata harkar kiwon lafiya a Afirka.
Wangendo, wanda ya bayyana hakan yayin taron musayar ra’ayoyi tsakanin manyan jami’an Sin da Afirka game da hadin-gwiwarsu ta fannin bunkasa ci gaba, wanda ya gudana a ranar Alhamis, ya ce a tsawon shekaru da dama da suka gabata, Sin ta ci gaba da tabbatar da aniyarta ta inganta kiwon lafiya a kasashen Afirka, musamman ta hanyar gina helkwatar cibiyar Africa CDC, wadda ta zamo alamar dake nuni ga karfin dangantakar Sin da kasashen Afirka.
- Tabbas Zai Yiwu A Kawo Ƙarshen Tashin Hankalin Da Ke Tagayyara Yara – Rahoton MDD
- MDD Ta Zartas Da Kudurin Kafa Yanayi Maras Shinge Ga Masu Bukata Ta Musamman
Jami’in ya kara da cewa, tallafin tsawon lokaci da Sin ke samarwa ta fuskar bunkasa sanin makamar aiki ga kwararrun jami’an kiwon lafiya dake Afirka, yana ci gaba da samarwa jami’an da gogewar da suke bukata, ta tunkarar kalubalolin lafiya na yanzu, da ma wadanda ake iya fuskanta a nan gaba.
Wangendo, ya ce irin wannan yunkuri na hadin kai, baya ga tabbatar da kimtsa Afirka ta fuskar tunkarar kalubalolin lafiya na yau, yana kuma baiwa nahiyar damar jure barazanar da ka iya bullowa ba tsammani a nan gaba. (Saminu Alhassan)