Yau Litinin, an kaddamar da shirin zantawa na hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaru na kasar Sin da na kasashen waje domin shirin bidiyo na “Yawo a Sin: Lardin Hainan mai kuzari”, da kuma taron kara wa juna sani na kafofin watsa labarai na “Abokan kungiyar ASEAN”, wanda cibiyar shirye-shiryen harsunan Asiya da Afirka ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da reshen ofishin CMG dake lardin Hainan suka shirya a cibiyar CMG ta birnin Sanya dake lardin.
A yayin bikin kaddamar da taron, babban mamban kwamitin jam’iyyar kwaminis ta Sin na lardin Hainan, Wang Bin, ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, a shekarun baya-bayan nan, an ci gaba da zurfafa hadin gwiwar cinikayya tsakanin Hainan da kungiyar ASEAN, inda aka samu karuwar ciniki tsakanin bangarorin biyu daga kasa da yuan biliyan 30 a shekarar 2021 zuwa yuan biliyan 57.91 a shekarar 2024.
Zhang Hui, mataimakiyyar darektar cibiyar shirye-shiryen harsunan Asiya da Afirka ta CMG, ta bayyana a jawabinta cewa, jerin shirye-shiryen tsara shirin “Yawo a Sin: Hainan mai kuzari”, ba wai kawai za su zama ababen koyi ga tsarin hadin gwiwar kafofin watsa labaru na “Abokai na kungiyar ASEAN” ba ne, har ma sun zama wani kuduri na hadin gwiwa ga gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da ASEAN.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp