An kaddamar da wani sabon babban filin wasa a birnin N’Djamena na kasar Chadi, wanda kasar Sin ta gina wa kasar kyauta.
Yayin bikin kaddamarwar da ya gudana ranar Juma’a, shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby, ya buga kwallon kafa da kansa, a matsayin alamar fara amfani da babban filin wasan.
Cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Deby ya gode wa kasar Sin, gami da bayyana filin wasan a matsayin daya daga cikin sakamakon da aka cimma, bisa huldar hadin kai, da mutunta juna, da ta kasance tsakanin kasashen Chadi da Sin.
Wani kamfanin kasar Sin ne ya gina babban filin wasan tare da mika shi ga kasar Chadi a ranar 12 ga wata. Girman filin wasan ya kai muraba’in mita dubu 33, wanda ya kunshi kujerun masu kallon wasanni dubu 30, da filayen wasan kwallon kafa, da na kwallon kwando, da dimbin na’urorin zamani daban daban. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp