A jiya Alhamis, an kaddamar da baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka da kuma baje kolin fasahohin injiniya na Sin karo na 18 a Abuja na Najeriya, inda jakadan kasar Sin dake kasar Najeriya Mr. Yu Dunhai ya halarta tare kuma da bayar da wani jawabi.
A cikin jawabinsa, jakada Yu ya ce, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar aiki a Sin tare da halartar taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC a watan Nuwamba, inda shugabannin kasashen biyu suka cimma muhimmiyar matsaya yayin ganawarsu. Sun kuma sanar da daga dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa kyakkyawar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, wadda ta inganta dangantakar Sin da Najeriya zuwa sabon matsayi a tarihi, ta kuma zana sabon tsari ga ci gaban dangantaka tsakanin kasashen biyu, da kuma samar da sabon yanayi ga hadin gwiwa mai amfani tsakanin Sin da Najeriya.
Baje kolin na wannan karo muhimmin aiki ne wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a dandalin FOCAC da ganawar shugabannin kasashen biyu, wanda zai ci gaba da inganta masana’antu da zamanantar da aikin noma na Najeriya, da kuma sa kaimi ga zurfafa hadin gwiwar kasashen biyu a fannoni daban daban. (Safiyah Ma)