An kaddamar da bikin baje koli na aikin noma da albarkatun dabbobi na kasa da kasa karo na 7 na kasar Cote d’Ivoire a cibiyar bukukuwan baje koli ta kasa da kasa dake birnin Abidjan, a jiya Jumma’a 23 ga wannan watan.
A matsayin muhimmiyar bakuwar kasa a gun bikin baje kolin, kasar Sin ta kafa rumfarta a tsakiyar cibiyar, inda aka gwada fasahohin zamani na aikin noma da injuna na kasar Sin.
Firaministan kasar Cote d’Ivoire Robert Beugre Manbe, ya bayyana a yayin bude bikin cewa, kasar Sin tana kan gaba a duniya a fannin fasahohin zamani na aikin noma. Kuma kasar Cote d’Ivoire za ta ci gaba da yin kirkire-kirkire kan fasahohin zamani don sa kaimi ga zamanantar da aikin noma a kasar da kuma inganta karfinta a wannan fanni.
Mataimakin ministan harkokin aikin noma da raya kauyuka na kasar Sin Zhang Xingwang, ya bayyana cewa, kasar Cote d’Ivoire ta fi samar da cocoa da dan yazawa (cashew nuts) da roba da sauran amfanin gona, kuma kasar Sin tana da babbar kasuwa, don haka bangarorin biyu suna da kyakkawar makoma kan hadin gwiwar fasahohin aikin noma, da samar da amfanin gona, da tattalin arziki da cinikayya da sauransu. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp