Yau Talata a nan birnin Beijing, a karo na farko CMG tare da hadin gwiwar ma’aikatar al’adu da yawon shakatawa ta kasar Sin suka kaddamar da bikin baje kolin fina-finai na kasar Sin ga duniya.
Yayin bikin, darurruwan kafofin yada labarai na kasa da kasa za su gabatar da fitattun fina-finai fiye da 50 da CGTN ta gabatar cikin harsunan Turanci da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da harshen Rashanci.
A jawabin da ya gabatar, mataimakin shugaban hukumar yayata ayyuka na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kana shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, wadannan fina-finai fiye da 50 za su nunawa duniya labaran al’ummar Sinawa na neman cimma burinsu, ta yadda al’ummar duniya za su fahimci zaman rayuwar al’ummar Sinawa.
Yana mai fatan, ta hanyar amfani da wannan dandali mai kyau za a kara tuntubar al’ummar duniya da yin mu’ammalar al’adu da hadin kai a fannoni daban-daban, zai samar da wata gada ta sadarwa tsakanain al’ummomin kasashen duniya da yin mu’amalar al’adu da hadin gwiwa na zahiri, da rubuta wani sabon babi na mu’amala da hadin gwiwa kan wayin kan duniya.
A yayin bikin budewar, mahalarta fiye da 100 daga kasashe da yankuna fiye da 60 da suka hada da kasashen Jamus da Faransa da Rasha da Najeriya da Tanzaniya sun bayyana kyakkyawar fatansu cikin harsuna 18. (Amina Xu)