Jami’ar Dar es Salaam ta kasar Tanzania da jami’ar Zhejiang Normal ta kasar Sin, sun yi hadin gwiwar kafa cibiyar hadin kai ta Sin da nahiyar Afirka, don raya ilimin dijital, a wani mataki na samar da zarafin dunkule bayanai da fasahohin sadarwa ko ICT domin daliban Afirka.
An gudanar da bikin kaddamar da cibiyar ne a jiya Laraba uku ga watan nan na Satumba, a harabar jami’ar Dar es Salaam, kuma bikin ya hallara jami’an gwamnati, da malamai, da abokan hulda na kasa da kasa, wanda hakan ke nuni ga himmar sassan biyu wajen bunkasa ilimin dijital a Tanzania da ma sauran sassan Afirka.
Da yake tsokaci yayin bikin, shugaban tsangayar koyar da ilimin tarbiyya a jami’ar ta Dar es Salaam Nkanileka Loti Mgonda, ya ce cibiyar za ta karfafa damar malamai ta rungumar kirkire-kirkire, da karfafa hadin gwiwa a fannin koyar da ilimi.
Mgonda, ya ce ilimin dijital bai shafi samar da hidimomi kadai ba, fanni ne dake zama wata gada mai sada dalibai da ilimi, da kuma dunkule kasashen duniya waje guda.
Ya ce ana sa ran wannan sabuwar cibiya da aka kaddamar za ta kasance sansanin horarwa, da bincike, da hadin gwiwa tsakanin sassan duniya, kuma za ta samar da gudunmawar dunkulewa, da koyar da dabarun kirkire-kirkire a dukkanin sassan Afirka. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp