• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kaddamar Da Ginin Sabuwar Hedikwatar Kungiyar ECOWAS

by CMG Hausa
3 years ago
ECOWAS

A jiya Lahadi ne aka aza tubalin ginin sabuwar hedikwatar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yankin Afirka ta yamma ko ECOWAS, a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, aikin da kasar Sin za ta tallafa wajen gudanar da shi.

Ana sa ran ginin zai baiwa kungiyar damar tattare ayyukanta wuri guda, sabanin yadda a yanzu kungiyar ke da ofisoshi 3 a birnin Abuja.

  • Jihar Kebbi Zata Samu Tallafin Dala 350,000 – ECOWAS 

Shugabannin kasashen yammacin Afirka, ciki har da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, da takwarorinsa na Guinea Bissau da Saliyo, da kuma shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS Omar Alieu Touray, da jakadan Sin a Najeriya Cui Jianchun, su ne suka jagoranci bikin aza tubalin ginin sabuwar hedikwatar.

Da yake tsokaci yayin kaddamar da aikin, jakada Cui Jianchun ya ce daukar nauyin ginin sabuwar hedikwatar ta ECOWAS da Sin ta yi, na nuni ga irin goyon bayan kasar ga ayyukan kungiyar, da ma kawancen gargajiyar dake tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka.

A nasa jawabin kuwa, shugaba Buhari ya bayyana aikin a matsayin shaidar goyon bayan Sin ga ECOWAS, kuma bayan kammalarsa, zai zamo matsugunin manyan ofisoshin ECOWAS 3, da suka hada da sakatariyar kungiyar, da kotun kasashe mambobin kungiyar, da kuma majalissar dokokin ECOWAS.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

Buhari ya kara da cewa, aikin da kamfanin kasar Sin zai gudanar, zai zamo masaukin kasashen yankin yammacin Afirka baki daya, wanda zai wakilci hadin kai da ’yan uwantaka tsakanin kasashe mambobin kungiyar, zai kuma alamta karin aniyar mambobin kungiyar game da samar da ci gaba da dinkewar yankin.

Shi kuwa shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS Omar Alieu Touray cewa ya yi, wannan rana ce mai muhimmancin gaske a tarihin kungiyar ECOWAS. Ya kuma jinjinawa gwamnatin kasar Sin bisa goyon bayanta ga kungiyar.

Alieu Touray ya kara da cewa, sabuwar hedikwatar za ta baiwa hukumar gudanarwar ECOWAS, damar karbar bakuncin daukacin jami’anta a wuri guda, ta yadda hakan zai inganta ayyukanta, da rage tsadar kudaden gudanarwa, da cimma karin nasarorin aiki. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya

October 10, 2025
Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal
Daga Birnin Sin

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

October 9, 2025
Next Post
PDP Ta Nada Yakubu Dogara A Matsayin Mamba A Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

PDP Ta Nada Yakubu Dogara A Matsayin Mamba A Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya

Sin Ta Gabatar Da Shawarwari Shida Game Da Karfafa Tsarin Shari’a Da Inganta Shugabanci A Duniya

October 10, 2025
Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya

Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya

October 10, 2025
Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

October 10, 2025
Nijeriya

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
ECOWAS

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.