Bisa labarin da hukumar ikon mallakar fasaha ta kasar Sin wato CNIPA ta bayar, an ce, hukumar CNIPA da kungiyar kula da ikon mallakar fasaha ta yankin Afirka wato ARIPO sun tsai da kuduri tare, na kaddamar da gwajin tsarin binciken kayayyaki masu lambar kira na Sin da Afirka cikin gajeren lokaci wato PPH a yau 8 ga wannan wata, wa’adin aikinsa ya kai shekaru 5, wato har zuwa ranar 7 ga watan Yuni na shekarar 2029.
Wani jami’in hukumar CNIPA ya bayyana cewa, tsarin ya kasance matakin yin bincike kan kayayyaki masu neman lambar kira na kasa da kasa da yankuna cikin gajeren lokaci, an rage tsawon lokacin yin binciken ta hanyar gudanar da ayyuka masu ruwa da tsaki tsakanin hukumomi daban daban. Tun daga watan Nuwamban shekarar 2011 da aka kaddamar da tsarin har zuwa yanzu, hukumar ta CNIPA tana hadin gwiwa tare da takwarorinta daga kasashe ko yankuna 32 a wannan fanni. (Zainab Zhang)