An kaddamar da kawancen masana’antun raya tattalin arzikin ayyukan da suka shafi sufurin jiragen fasinja da marasa matuka dake zirga-zirga maras nisa daga doron kasa na Beijing-Tianjin-Hebei, jiya Asabar a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda aka rattaba hannu kan ayyuka 33 masu ruwa da tsaki.
Ayyukan sun kunshi gina wajen samar da babban tsarin masana’anta na samar da batura marasa daukan zafi da wurare masu ruwa da tsaki da fasalin hanyar zirga-zirgar ababen hawa masu tafiya a sama maras nisa a wani yankin kimiyya da sauransu.
- Tirƙashi: Har Yanzu Wasu Ƴan Fansho Na Karɓar 500 A Wata
- Sojoji Sun Kashe Wasu ‘Yan Bindiga A Zamfara
Bikin kaddamarwar ya samu halartar baki daga biranen Beijing da Tianjin da lardin Hebei, inda suka kalli yadda wani jirgi mara matuki ya gwada zirga-zirga mara nisa daga doron kasa da wasu dabarun kasuwanci a sararin sama.
Guo Kangwei, shugaban gundumar Baodi ta Tianjin, ya ce wannan bangaren tattalin arziki mai nasaba da sufurin ababen hawa masu tafiya a sama maras nisa daga doron duniya, misali ne na sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko kuma sabon jigon raya tattalin arziki. Haka kuma, wata sabuwar dabara ce ta raya harkokin masana’antu.
Ya ce, Baodi na kokarin inganta hadewar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da kirkire-kirkiren masana’atu da gaggauta raya jerin masana’antu masu alaka da tattalin arziki mai nasaba da sufurin ababen hawa masu tafiya a sama maras nisa daga doron kasa. (Fa’iza Mustapha)