An Kaddamar da Littafin da ya tattaro tarihin hamshakiyar Kasuwar tufafin Nan ta Kantin Shekara 556, asalin wannan Kasuwa ya somo ne daga Kasuwar kurmi, sakamakon yadda fatake ke kwararowa zuwa Kano domin saye da sayarwa daga kasashen Arewaci, Yammacin da gabashin Nijeriya.
Mawallafi Littafin Wanda Tsohon ma’aikancin Jaridar Gaskiya tafi kwabo ne Alhaji Muhammad Abdullahi (Mai Dubji) ya bayyanawa manema labarai cewa alokacin Sarki Muhammadu Rumfa ne aka samarwa wadannan baki masaukai a unguwanni Darma da dandalin Fagge, masu sauka a Unguwar dandalin Fagge ne suka kafa Kasuwar Kantin Kwari saboda wadataccen ruwa da Kuma ni’imar dake wannan wuri.
- Jawabin Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Game Da Sanya Hannun Amurka Kan Dokar Ba Da Izinin Tsaro Ta Kasa Ta Shekarar 2023
- Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin Max Air Ya Rasu
Alhaji Mai Dubji ya ce, ya takaita Littafin na farko ne domin ‘yan Kasuwa su samu sukunin dubawa tare da ganin tarihin wannan kasuwa, Haka suma Dalibai masu gudanar da bincike, wannan Littafi zai taimaka tare da saukaka masu hanyoyin samun bayanan wannan Kasuwa.
Shahararren dan Kasuwar nan Alhaji Salisu Musa Sambajo (MFR) (Sardaunan Alagodo na Jihar Legas) ne ya kaddamar da Littafin a wani salo inda aka kaddamar da Littafin ta yanar gizo.