A ran 2 ga watan nan, CMG ta kaddamar da shirin “Afirka a cikin fina-finai” zagaye na biyu wato bikin nune-nunen fina-finai da sauran ayyuka a jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing BFSU. An gayyato masu shirya fina-finai daga Najeriya da Tanzaniya da Habasha da Benin da sauransu, wadanda za su baje kolin fina-finan su guda 10 a jami’o’in kasar ta Sin, ban da jami’ar BFSU, za kuma su kai ziyara a jami’ar koyar da ilmin watsa labarai ta kasar Sin da jami’ar nazarin harkokin sufuri ta birnin Xi’an da jami’ar Sichuan.
Ofisoshin jakadancin Sin dake kasashen Afirka daban-daban na goyon baya shirin nan. Jakadan Sin dake Najeriya Dun Hai ya ce, yana farin ciki da ganin an nuna fina-finai 3 daga Najeriya a jami’o’in kasar Sin, matakin da zai karawa matasa Sinawa sani da fahimtar al’adun Afirka, wadanda za su burge su da kuma samu karbuwa daga wajensu sosai. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp