Kafin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke yi a kasar Rasha, an kaddamar da shirin bidiyo mai taken“Bayanin magabata da Xi Jinping ke so” na biyu da harshen Rashanci a wasu manyan gidajen talabijin na kasar ta Rasha.
A yau Litinin 20 ga wata, mataimakin shugaban sashen fadakar da jama’a na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Shen Haixiong, da shugaban gidan talabijin da rediyo na kasar Rasha Oleg Dobrodeev ne suka kaddamar da shirin, kana suka gabatar da jawabai tare.
Bangarorin biyu sun bayyana cewa, za su taka muhimmiyar rawar da ta kamata a fannin watsa labaru, da sa kaimi kan shawarar wayewar kai a duniya, da karfafa yin mu’amala, da fahimtar juna tsakanin Sin da Rasha, da cudanya tsakanin jama’ar kasashen biyu, da kuma inganta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp