An kaddamar da taro na 10 na zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a yau 1 ga watan Maris a nan birnin Beijing, inda memban hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban majalisar CPPCC Wang Huning ya halarci taron.
A gun taron, an zartas da kudurin gudanar da zama na 3 na majalisar CPPCC karo na 14 a ranar 4 ga wannan wata a birnin Beijing, an kuma gabatar da shawara kan ajendar zaman, wato sauraro da yin bincike kan rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar CPPCC da yadda aka gudanar da ayyukan da aka cimma daidaito a kai, a gun zama na 2 na majalisar CPPCC karo na 14, da halartar zama na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, da kuma sauraro da tattaunawa kan aikin gwamnatin kasar da sauran rahotanni. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp