Yau Asabar ne aka kaddamar da taron koli, na raya fasahar sadarwar zamani na kasar Sin karo na 5, a birnin Fuzhou dake kudancin kasar Sin.
Memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar, Mista Huang Kunming, ya halarci bikin bude taron ta kafar bidiyo, inda ya yi jawabin cewa, ya dace a kara nazari, tare da daukar matakan zahiri, don tabbatar da muhimmin ra’ayin shugaba Xi Jinping na kasar, dangane da gina kasar Sin mai karfin harkokin yanar gizo ta Intanet, da gaggauta bunkasa sana’o’in da suka shafi fasahar sadarwar zamani, don kara kawo sauye-sauye ga hanyoyin kere-kere, da rayuwa, da mulki da sauransu.
Huang ya kuma jaddada cewa, ya kamata a yi amfani da sabbin damammaki, da shawo kan sabbin kalubaloli, a lokacin da ake samun ci gaban fasahar sadarwar zamani. (Murtala Zhang)