A daidai lokacin da zaben 2023 ke kara karatowa, Kungiyar ‘Arewa Mobement for Good Gobernance’ (AM2G), ta kaddamar da wata yarjejeniyar samar da nagartaccen mulki a arewacin Nijeriya a hukumance da kuma karfafa hakuri da hadin kai tsakanin Muslmai da Kirista.
Yarjejeniyar ta gudana ne a lokacin kaddamar da gabatar da wani littafi mai suna Ka’idojin Jagoranci Tsakanin Addinin Musulunci da Kiristanci a Kaduna.
- Ina So Na San Siffofin Jinin Haila?
- Kamfanin Sin Ya Kammala Aikin Gina Tashar Samar Da Lantarki Ta Ruzibazi A Burundi
Shugaban kungiyar, Dakta Usman Bugaje ya bayyana cewa rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da sauran matsalolin da yankin arewacin kasar nan ke fama da su ne ya sa yarjejeniyar ta aiwatar da dokar tabbatar da hadin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci domin yakar munanan shugabanci.
Dakta Bugaje ya lura cewa babban abin da yarjejeniyar ta fi mayar da hankali a kai shi ne, yin amfani da hadin kai don neman shugabanci nagari daga shugabannin siyasa don ci gaban zamantakewar al’umma da ingantuwar tattalin arzikin yankin.
Ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su hada kai da cibiyoyin addini da na gargajiya domin cimma burinsu.
Dakta Bugaje ya kuma yi kira ga ‘yan arewa da su koma kan teburin shawara don sake tsara abubuwan da suka dace domin a ci gaba da rayuwa.