Yau Juma’a, aka kafa cibiyar nazari na babban rukunin gidan rediyo da talibiji na kasar Sin (CMG) a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Inda shugaban kamfanin CMG, mista Shen Haixiong, da shugaban cibiyar nazarin harkokin rayuwar al’umma ta kasar Sin kuma shugaban cibiyar nazarin tarihin kasar, mista Gao Xiang, suka halarci bikin kaddamarwar, tare da gabatar da allunan cibiyar nazarin, gami da tashar masu neman matsayin shaidar ilimi na Postdoctor, duk a karkashin CMG. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp