Da safiyar yau Talata da misalin karfe goma, an ga alamar adadin iskar gas da ya zarta cubic mita biliyan 50 wato ya kai cubic mita biliyan 50.06 a allon lantarki dake cibiyar jagorancin aikin samar da iskar gas ta filin hakar man fetur na Changqing na kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, an kafa babban yanki na farko wanda ke samar da iskar gas da yawansa ya kai cubic mita biliyan 50 a ko wace shekara a kasar Sin.
Bisa matsayinsa na cibiyar samar da iskar gas mafi girma a kasar Sin, filin hakar man fetur na Changqing yana samar da iskar gas ga jihohin Ningxia da Mongolia ta gida, da biranen Beijing da Tianjin, da lardin Hebei, haka kuma yana samar da iskar gas ga birnin Shanghai, da lardunan Zhejiang da Jiangsu da Guangdong, da kuma yankunan musamman na Hong Kong da Macau. Ana iya cewa filin Changqing yana taka babbar rawa kan aikin raya tattalin arzikin kasar Sin ba tare da gurbata muhalli ba.
Kawo yanzu gaba daya adadin iskar gas da filin Changqing ya samar ya riga ya kai cubic mita biliyan 555.
A cikin ‘yan shekarun baya bayan nan, filin Changqing yana ci gaba da kokari domin cimma burin tabbatar da masana’antu irin na zamani ta hanyar amfani da sabbin fasahohin zamani, kuma ya samu sakamako a bayyane. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)