Yayin da rashin tsaro da sace-sacen mutane a yankin Arewa maso yamma ya yi kamari musamman a jihar Zamfara, dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Aminu Ibrahim, mai wakiltar mazabar Kaura Namoda, ya shiga hannun ‘yansanda bisa zarginsa da hannu a garkuwa da mutane.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Muhammad Shehu Dalijan, ya tabbatar da cafke dan majalisar a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da wakilin Jaridar Daiiy Trust.
- Zanga-zanga: Za Mu Yi Amfani Da Dandalin Eagle Square Ko Da Izini Ko Babu A Abuja
- Sin Da Amurka Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna A Dukkanin Matakai
Ya kuma bayyana cewa, Hakimin Kaura Namoda, Alhaji Jafaru Abdullahi Kumburki da tsohon shugaban karamar hukumar, Nasiru Muhammad, suna hannun ‘yansanda bisa irin wannan zargi.
Kwamishinan ‘yansandan ya ce, ana binciken hakimai uku na Danjibga, Bukkuyum da Unguwar Gyauro a kananan hukumomin Tsafe da Bukkuyum bisa irin wannan zargi.
Shugaban ‘yansandan ya ci gaba da cewa, an kama Ibrahim, dan majalisa mai ci a majalisar dokokin jihar Zamfara bisa zarginsa da hannu wajen sace Alhaji Ibrahim Sarkin Fada mai shekaru 80 a kauyen Kasuwar Daji.