A kalla, rundunar jami’an tsaro na NSCD a jihar Kano ta samu nasarar kama mutum goma sha hudu, bisa zargin kokarin damfarar wadansu mutane.
Jami’an sun ce,sun kama mutanen goma sha hudu,sano wata sabuwar zambar da suka bullo da ita.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ta NSCD Adamu Zakari, ya bayyana haka yayin da yake zanta wa da ‘yanjarida a hedikwatar hukumar da ke Kano.
Mace bayar da canjin sabbin kudin na zuwa kai-tsate babban bankin Nijeriya, domin su canji su ta barauniyar hanya.
Ya ce, wadanda aka Kaman su ne, Alhaji Ubandi Hotoro da Haruna Yahaya, da Rabi’u Ibrahim, da Isma’ila Mohammad Umar da Nura Aminu da Nasiru Adamu da Nazef Lawal, mai shekara20.
Sauran su ne Sulaiman Tijjani da Mustapha Ismail Haruna da Aminu Jibril da Lawal Ibrahim da Abubakar Jibril da Abdullahi Hassan da Fatima Ibrahim.
Zakari ya tabbatar da cewa jami’an na NSCDC da DSS da CBN za su tabbatar da cewa, an hukunta wadanda aka Kaman matukar an same su da laifi.
Kamar yadda ya ce, “Za mu gudanar da bincike cikin tsanakim domin tattara hujjojin da za mu gabatar gaban kotu” In ji shi
Daya daga cikin wadanda aka Kaman Alhaji Ubandi Hotoro, ya ce ba a samu wani kayan laifi ba tare da shi.