Rundunar sojoji ta ‘Operation Hadin Kai’ ta kama sojoji 18 da ‘yansanda 15 da ake zargi da sayar da makamai ga wasu da ba su cancanta ba.
Wani jami’in rundunar, Manjo Ademola Owolana, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai game da tsaro da ayyukan rundunar hadin guiwa ta Arewa maso Gabas daga 2024 zuwa 2025 a Maiduguri.
- Gwamna Uba Sani Ya Kammala Titin Unguwar Su El-Rufai
- Mutum 1 Ya Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Abuja
Ya ce, an samu nasarorin ne a karkashin shirin ‘Operation Snowball’ wanda aka kaddamar a watan Agustan 2024 don dakile sace-sacen harsasai a tsakan jami’an rundunar.
Ya ce, ana gudanar da aikin binciken ne a fadin jihohi 11 inda aka kama wadanda ake zargin a Bauchi, Benuwe, Borno, Ebonyi, Enugu, Lagas, Filato, Kaduna, Ribas, Taraba da kuma babban birnin tarayya, Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp