A ranar Alhamis 5 ga watan nan ne aka gudanar da bikin kammala aikin tashar samar da wutar lantarki ta Busanga, da ke Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, wadda wasu kamfanonnin kasar Sin suka zuba jarin gina ta. Shugaban kasar Félix-Antoine Tshisekedi, ya halarci bikin, tare da yanke kyallen dake alamta kaddamar da tashar.
Da yake jawabi yayin bikin, ministan ruwa da albarkatun lantarki na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo Mwenze Mukaleng Olivier, ya bayyana cewa, wutar lantarki ita ce abin da kasar ke bukata. Kuma tashar samar da wutar lantarki ta Busanga, nasara ce ta hadin gwiwa da aka samu tsakanin kasarsa da Sin, kana za ta ba da gudummawa ga yunkurin zamanintar da kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
A nasa jawabin kuwa, jakadan kasar Sin a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, Zhao Bin, ya bayyana cewa, kasashen Sin da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, manyan kasashe ne masu tasowa, kuma suna bukatar juna sosai ta fuskar raya tattalin arziki, sun samu tushe mai fa’ida, da kuma tabbataccen hadin gwiwa. Ya ce ya yi imanin cewa, fasahar zamani, da na’urori masu inganci, da kwarewar da kasar Sin ta samu, da kuma isasshen jarin da kasar ta zuba, za su sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin Kongo. (Mai fassara: Bilkisu Xin)